Sanata Bernie Sanders ya yi kira ga al’ummar Amurka da kada su bari guguwar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar ta kawar da hankulansu daga babban bala’in da ke faruwa a Gaza.
“A yayin da yawancin kafofin watsa labarai suka mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar Amurka, dole ne mu ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a Gaza, inda mutane suke ci gaba da fuskantar bala’i da rashin jinƙai,” a cewar wata sanarwa da Sanders ya fitar.
Sanders ya ƙara da cewa Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙi kan Falasɗinawan Gaza ba tare da sassauci ba, yana mai zargin cewa Firaminista Benjamin Netanyahu “ya yi watsi da dukkan dokokin ƙasashen duniya sannan ya jefa rayuwar al’ummar Gaza cikin masifa”.
“Shi ya sa Netanyahu yake fuskantar tuhuma daa Kotun Hukunta Manyan Laifka ta Duniya,” in ji Sanders.
Sanatan wanda ke takara a matsayin ɗan indifenda ya ce Amurka tana ci gaba da kashe biiliyoyin dala don taimaka wa Isra’ila sannan tana ba ta bama-bamai da makamai don ci gaba da yaƙi a Gaza.
“Mu, Amurkawa, muna da laifi a wannan ta’asa,” in ji Sanders, sannan ya yi kira ga Amurka ta daina taimaka wa “yaƙin da Netanyahu yake yi”.