Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 15 A Wani Hari Kan Makarantar MDD

Rahotanni daga Falasdinu na cewa sojojin Isra’ila sun kai hari kan wata makarantar da MDD ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu (UNRWA) a sansanin

Rahotanni daga Falasdinu na cewa sojojin Isra’ila sun kai hari kan wata makarantar da MDD ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu (UNRWA) a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da jikkata wasu.

Makarantar ta UNRWA, wacce ke dauke da daruruwan mutanen da suka rasa matsugunai, an kai ma ta harin ne yau Lahadi, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan matsugunai, makarantu, da cibiyoyin UNRWA a fadin yankin da aka yi wa kawanya.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa, harin da aka kai a makarantar Abu Oreiban da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat ya kashe mutane 15 tare da jikkata 80.

“Wannan kisan kiyashi ya zo ne a matsayin ci gaba da kisan kiyashi da sojojin mamaya ke yi a kan al’ummar Palastinu a wata na goma a jere,” in ji sanarwar.

Tun da farko majiyoyin likitocin Falasdinawa sun ce akalla fararen hula 15 ne suka mutu sannan wasu 70 suka jikkata sakamakon harin bam da Isra’ila ta kai a makarantar.

Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza duk da yunkurin da ake na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kasashen Amurka da Qatar da kuma Masar ke yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments