Babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell, ya yi kakkausar suka dangane da wani kazamin harin da Isra’ila ta kai zirin Gaza a baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 90 da suka hada da mata da yara tare da jikkata wasu fiye da 300, a yankin Al-Mawasi da ke Khan Yunis, a kudancin Gaza.
Mista Borrell ya bayyana hakan ne ta hanyar wani sako a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa harin na Isra’ila ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama dake wurin da ya kamata ya zama mai aminci.
Ya bayyana cewa Yake-yake suna da iyaka da dokokin kasa da kasa suka tanada; muna Allah wadai da duk wani tashin hankali.”
Borrell ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, da kuma kawo karshen mummunan halin da fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba suke ciki a Gaza.
Harin ya zo ne a rana ta 281 na yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, tun bayan harin ba-zata na kungiyar Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba.
Hare-haren na Isra’ila sun yi sanadin rayukan Falasdinawa 38,345 a Gaza, galibi fararen hula, a cewar bayanai daga ma’aikatar lafiya ta Gaza.