Wata kasar Larabawa ta sayi tauraron dan adam na leken asiri kirar haramtacciyar kasar Isra’ila kuma ta aika da tawaga zuwa Isra’ila
Wasu kafafen watsa labarai sun watsa rahoton yadda kasar Moroko ta sayi tauraron dan Adam na yahudawan sahayoniyya da ya kai kimar kudi dala biliyan daya, a wata yarjejeniya da aka kulla a lokacin bazara na shekara ta 2023 kuma aka sanar da yarjejeniyar a watan Yunin da ya gabata.
Kasar Moroko ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin masana’antan sararin samaniyar haramtacciyar kasar Isra’ila na kudi dalar Amurka biliyan daya, kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila da na Faransa suka ruwaito.
A cewar jaridar Times of Isra’ila, ta yahudawan sahayoniyya, Amir Peretz, shugaban kamfanin masana’antun sararin samaniyar haramtacciyar kasar Isra’ila kuma tsohon ministan yaki, tattalin arziki da masana’antu, mai yiwuwa ya tafi kasar Moroko a asirce a cikin ‘yan kwanakin nan don daidaita yarjejeniyar.