Jami’an Tsaron Kasar Iran Sun Cafke Madugun ‘Yan Ta’addan Birnin Kerman Na Kasar

Jami’an tsaron kasar Iran sun yi nasarar cafke madugun ‘yan ta’addan birnin Kerman na kasar Iran a wajen kasar A cikin wata sanarwa da ma’aikatar

Jami’an tsaron kasar Iran sun yi nasarar cafke madugun ‘yan ta’addan birnin Kerman na kasar Iran a wajen kasar

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar Iran ta fitar a jiya Asabar, ta tabbatar da kame wanda ya shirya harin ta’addancin birnin Kerman mai suna Abdullah Queyta.

Tun daga ranar 21 ga watan Mayun da ya gabata har zuwa ranar 5 ga watan Yuli, sashin yaki da ta’addanci a ma’aikatar tsaron kasar Iran ya gano wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda da kuma wasu kararraki 79 da suke bukatar murkushe ‘yan ta’addan kai tsaye, don haka jami’an tsaron kasar suka jagoranci wani farmaki a kansu, tare da kame dimbin ‘yan ta’adda da kayan aikin leken asiri da makamai.

Sanarwar ta ma’aikatar ta kara da cewa: A jerin ayyukan da ta gudanar, baya ga gano gungun ‘yan ta’addan da suka shigo cikin kasar Iran a kwanan nan tare da cafke su, kuma an gano wasu gungun ‘yan ta’adda da dama da a baya-bayan nan suka shigo cikin kasar domin jagorantar ayyukan ta’addanci ko kuma kai hare-haren kunar bakin wake. Sanarwar ta ci gaba da cewa: Daya daga cikin muhimman nasarorin da aka cimma a baya-bayan nan shi ne kame daya daga cikin manyan shugabannin ‘yan ta’adda da ke shiryawa da bada umurnin aiwatar da ayyukan ta’addanci a birnin Kerman mai suna “Abdullah Queita”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments