Kasar Iran Ta Yi Tsokaci Kan Ayyukan Ta’addancin Yahudawan Sahayoniyya ‘Yan Mamaya

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tsokaci game da laifukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a garin Khan Yunus na Falasdinu Kakakin ma’aikatar harkokin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tsokaci game da laifukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a garin Khan Yunus na Falasdinu

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani da yake tsokaci kan kisan gillar birnin Khum Yunus, ya jaddada cewa: Kai hare-haren wuce gona da iri kan tantunan ‘yan gudun hijira a yankunan da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suka bayyana su a matsayin amintattun yankuna da suke rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, wani sabon laifi ne da tarihin zai kirgo su a cikin muggan laifukan yahudawan sahayoniyya.

Kan’ani ya kara da cewa: Yahudawan sahayoniyya sun sake nuna ta’asarsu da wannan aika-aika tare da tabbatar da cewa ba su tsaya ga wani jan layi ba dangane da kimar bil’adama a kokarinsu na boye gazawarsu a filin daga.

Ya kuma jaddada cewa laifukan yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da gudana karkashin cikakken goyon bayan Amurka sakamakon shirun da kasashen duniya suka yi, inda suke ci gaba da kashe fararen hula ba ji ba gani, ga kuma siyasar munafunci na kasashen Turai.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kuma nanata muhimman ayyukan kotun duniya da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa a cikin shari’a kamawa da gudanar da shari’a kan ‘yan sahayoniyya masu nuna wariyar al’umma.

Kan’ani ya yi kira ga dukkan kasashe musamman na musulmi, da kuma ‘yantattu na duniya da su gaggauta gurfanar da shugabannin yahudawan sahayoniyya masu aikata muggan laifuka a gaban kuliya ta hanyar bin diddigin shari’ar kasa da kasa tare da sanya musu cikakken takunkumi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments