NANS: Cire Tallafin Mai A Najeriya Bai Haifar Da Da Mai Ido Ba

Kungiyar Daliban Najeriya (NANS), ta shaida wa Shugaba Bola Tinubu cewa matsalar man fetur na ƙara ta’azzara a Najeriya, kuma cire tallafin bai haifar da

Kungiyar Daliban Najeriya (NANS), ta shaida wa Shugaba Bola Tinubu cewa matsalar man fetur na ƙara ta’azzara a Najeriya, kuma cire tallafin bai haifar da ci gaban da ake tsammani ba.

NANS, ta ce cire tallafin ya jawo matsaloli masu yawa ga ’yan Najeriya kuma ya haifar da ƙarancin man fetur maimakon wadatarsa.

Sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Abdul-Yekinn Odunayo, magatakardar ƙungiyar, ya fitar a Abeokuta a ranar Asabar.

“Wannan matsala ba kawai tattalin arziƙi ta ke cutarwa ba, har ma tana shafar jin daɗin ɗalibai da karatunsu a faɗin ƙasar na. ’Yan Najeriya na fuskantar ƙalubale sosai wajen samun man fetur.

“Akwai dogayen layuka a gidajen mai a ko ina, duk da alƙawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na cewa samun tsaikon mai zai ƙare. Amma hakan ba ta samu ba.

“Tsadar man fetur ta sa farashin sufuri ya ƙaru sosai, kuma ya haifar da tsadar kayan masarufi. Wannan tsadar na ƙara ta’azzara komai.

“Abin takaici ne cewa shekara ɗaya bayan cire tallafin, matsalar man fetur ta ƙara ta’azzara, kuma kamar ba a son ƙasar nan ta ci gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments