Gwamnatin Sudan: Abin da ya faru a Geneva ya saba wa shawarwarin Jeddah

Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa, bisa la’akari da irin aikin da nauyin da take da shi na wajibcin kiyaye dokokin jin kai na kasa

Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa, bisa la’akari da irin aikin da nauyin da take da shi na wajibcin kiyaye dokokin jin kai na kasa da kasa, da kuma kishinta na hadin gwiwa da kyakkyawar alaka da MDD, ta amince da shiga Tattaunawar a birnin Geneva na kasar Switzerland game da halin da ake ciki na jin kai.”

A cikin wata sanarwar da manema labarai da ta fitar, dangane da kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na yin shawarwari kai tsaye a birnin Geneva, dangane da halin da ake ciki, gwamnatin ta sanar da cewa, “Kwamishiniyar Agajin Gaggawa, Madam Salwa Adam Benya, ita ce ta jagoranci tawagar kwararrun da ke wakiltar gwamnatin  Sudan a wadannan shawarwari, kuma tawagar ta hada da wakilan ma’aikatu daban-daban.”

Sanarwar da manema labarai ta fitar ta bayyana cewa, duk da gayyatar da wakilin na musamman ya gabatar, amma tawagar gwamnatin Sudan, kwanaki kadan bayan isar ta a Geneva, ba ta samu ba bayani kan ajanda ko shirin da ake das hi na gudanar da  waɗannan shawarwari ba.

Sanarwar ta bayyana cewa, an bukaci tawagar da ta je Geneva, sabanin yadda ake tattaunawa a kan batutuwa irin wadannan,  lamarin da tawagar gwamnatin ba ta ganinsa a matsayin kira da ya dace a hukumance, kuma ya sabawa fahimtar kaidoji na tattauwa bisa tsari na kasa da kasa.

A halin da ake ciki, gwamnatin Sudan ta tabbatar da cewa “ba ta ga bukatar kafa wani sabon dandalin shiga tsakani,” tana mai jaddada cewa tana nan a kan shawarwarin  Jeddah da alkawuran da ta dauka, da kuma wajibcin aiwatar da wadannan alkawurran da aka aka amince za a aiwatar da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments