Hukumomin mulkin soji na kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da suka hade a cikin sabuwar kungiyar hadin kan yankin Sahel (AES), sun yi tir da abinda suka kira shishigi na kungiyar Tarayyar Afirka a al’amuran cikin gidan kasashensu biyo bayan wani jami’in kungiyar ta AU, ya soki matakin ficewarsu daga ECOWAS.
“Kwamishanan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na AU, wanda yake magana a madadin shugaban hukumar AU, ya ce [a taron ECOWAS na ranar 8 ga watan Yuli a Abuja]: “Ficewar kasashen uku (…) ba abu ne da kungiyar ta AU ta amince da shi ba, kuma mun yi imani da ECOWAS guda daya,”
A cikin sanarwar manema labarai da suka fitar kasashen na AES sun ce “Wannan furicin abin mamaki ne kamar yadda ba a saba gani ba daga bangaren jami’in doka wanda ayyukansa ba su ba shi damar yin katsalandan a cikin harkokin cikin gida na kasashe membobin kungiyar ta AU ba.
kasashen uku, na kimanta duk wani maratani kan matakinsu na barin ECOWAS “a mastayin tsoma baki a cikin harkokin cikin gida” na AES.
ECOWAS dai ta yi gargadin a ranar 7 ga watan Yuli cewa yankin yammacin Afirka na fuskantar hadarin “raguwa” bayan da aka kafa kungiyar “AES”. Har ila yau, ana fuskantar tashe tashen hankula daga masu ikirarin jihadi, da samar da kudade da kuma matsaloli wajen samar da rundunar yankin.
Shugabannin gwamnatocin mulkin soji na kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun ce ba za su koma lungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ba, saidai kungiyar ta wakilta shugaban Senegal, domin shiga tsakani da nufin shayo kan kasashen.