An Yi Yunkurin Kashe Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump A Lokacin Yakin Neman Zabe

An yi yunkurin halaka tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hanyar harbinsa da bindiga a yayin yakin neman zabe Rahotonni sun bayyana cewa: Lamarin

An yi yunkurin halaka tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hanyar harbinsa da bindiga a yayin yakin neman zabe

Rahotonni sun bayyana cewa: Lamarin harbin tsohon shugaban na Amurka Donald Trump ya haifar da firgici a fagen siyasar Amurka, musamman ganin yadda ya bar fagen yakin neman zaben cikin jini.

Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa: An yi yunkurin kashe tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ne, a lokacin da yake jawabi gabanin wani gangamin zabe a jihar Pennsylvania.

Ba zato ba tsammani tsohon shugaban na Amurka ya dakatar da jawabin nasa yayin wani gangamin zabe a jihar Pensylvania a yammacin ranar Asabar, kuma an ji karar harbe-harbe a daidai wannan lokacin.

Hotunan faifan bidiyo sun nuna Trump yana buya a karkashin dandalin da yake gabatar da jawabin yayin harbin. Bayan haka, Trump ya bayyana a cikin masu gadin sa, yana rera waka a tsakanin magoya bayansa, fuskarsa cike da jini.

Tsohon shugaban na Amurka Donald Trump ya ce yana cikin koshin lafiya bayan an harbe shi, ofishin kamfen na Trump ya fada a cikin wata sanarwa a daren jiya wayewar garin yau Lahadi cewa: Shugaba Trump ya gode wa jami’an tsaro da masu ba da amsa na farko kan matakin da suka dauka cikin gaggawa yayin wannan danyen aikin.

Ofishin kamfen din na Trump ya kara da cewa: Trump yana cikin koshin lafiya kuma ana duba lafiyarsa a wata cibiyar kula da lafiya. Sannan za a fitar da karin bayani daga baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments