Martanin Wasu Shugabannin Kasashen Duniya Kan Yunkurin Hallaka Trump

Shugabanni da gwamnatocin kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani game da yunkurin hallaka tsohon shugaban Amurka Donald Trump. Harbin da aka yi

Shugabanni da gwamnatocin kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani game da yunkurin hallaka tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

Harbin da aka yi wa Trump, dan takarar shugabancin Amurka mai zuwa, a lokacin da yake gangamin yakin neman zabe ya fuskanci martani da dama musamman daga shugabannin kasashen duniya.

Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya ce ya damu matuka da harin da aka kai wa abokina.

Modi ya ce “Tashin hankali ba shi da gurbi a siyasa da dimokuradiyya.”

Shi ma firaministan Japan Fumio Kishida ya yi magana game da harin, yana mai cewa “dole ne mu tsaya tsayin daka kan duk wani nau’i na tashe-tashen hankula da ke kalubalantar demokradiyya.”

Anthony Albanese na Ostireliya ya ce ya kadu matuka da munanan al’amuran da suka faru a taron yakin neman zaben Trump, yana mai bayyana jin dadinsa da cewa tsohon shugaban na Amurka yana cikin koshin lafiya.

Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce shi da matarsa ​​Sara “sun kadu da harin da aka kai wa Shugaba Trump”.

“Muna yi masa addu’ar samun lafiya da samun sauki cikin gaggawa,” in ji Netanyahu.

Sauran shugabannin da suka nuna jin takaici game da lamarin sun hada dana Faransa, Turkiyya, China, da firaministan Biritaniya.

Shi kuwa shugaban Amurka, Joe Biden, ya bayyana farin ciki da jin cewa abokon hamayyarsa Donald Trump yana cikin koshin lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments