Zamanin Annabi Shaho: Siyasar Amurka Ta Amfani Da Karfi A Alakar  Kasa Da Kasa

Donald Trump wanda ya gina siyasarwa ta waje akan taken: “Bai Wa Amurka Fifiko” bai yi Imani da wata ka’ida ta doka, ko wani halin

Donald Trump wanda ya gina siyasarwa ta waje akan taken: “Bai Wa Amurka Fifiko” bai yi Imani da wata ka’ida ta doka, ko wani halin kwarai da zai dogara da su, wajen daukar matakan da yake son a fagen siyasar kasa da kasa.

Ana iya kwatanta yadda Donald Trump ya bude Zangon shugabancin na yanzu da yin maganganu da suke nuni da manufarsa ta cin kasashe da yaki, da irin salon zamanin mulkin mallaka, ko ma wanda ya gabaci rubutawa duniya abinda ake kira da dokokin kasa kasa. Ya fara mulkinsa ne da Magana irin cewa; ” ya kamata ace kasar Canada ta zama Jahar Amurka ta 51″, ya kuma kara da cewa;”  Iyakar dake tsakanin Canada Amurka kirkirarriya ce, ba ta gaske ba ce. A dalilin haka, abinda zai fi dacewa shi ne wannan kasar ta zama wani  bangare na kasar Amurka”.

Abinda ya biyo bayan hakan shi ne, bayyana aniyarsa na son ganin Amurkan ta shimfida ikonta akan yankin Greenland, ko dai ta hanyar sayen yankin ko kuma ta amfani da wasu hanyoyi. Ya bayyana cewa kasar Amurkan tana a bukatuwa da yankin saboda dalilai na tsaro da siyasa.

Ya fadi hakan ne ba tare da ya damu da cewa, kasar Canada da kuma kasar Denmark- da Greenland ke karkashinta ba- mambobi ne a cikin  kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.

A mataki na  gaba, shugaban kasar ta Amurka ya bayyana kwadayin kwace iko da mashigar ruwa ta “Panama”, shi ma bisa dalilai na manyan manufofin Amurka.

Wasu kafofin ma sun bayyana cewa, Trump ya bayyana kwadayin ganin cewa kasar Amurka ta shimfida ikonta akan kasashen Mexico da Cuba.! Ya fada wa wadannan kasashen cewa; “Muna nan tafe gare ku”.!

Da dama daga cikin masu bin diddigin harkokin siyasa  sun dauki  abinda Donald Turmp ya rika fada a matsayin  zance na ta fatar baki kawai, kuma ba ta wuce neman tsokana da jan hankali, amma daga lokacin da su ka ga shugaban kasar na Amurka ya sa an  kai kamo shugaban kasar Venezuela an kai shi Amurka sun gaskata cewa, lallai shi dan daba ne mai lasisi na kasa da kasa. Abinda ya aikata a kasar Venezuela yana nufin  take dokokin kasa da kasa.

 Anan yana da kyau a yi ishira da cewa, jinsin bil’adama ya dauki karnuka uku cikakku,wato tun bayan da aka Shata iyakokin kasashe, daga tsakiyar karni na 17 zuwa tsakiyar karni na ashirin,  aka iya cimma matsaya akan dokokin da za a yi amfani da su a tsakanin dukkanin kasashe. A karkashin wadannan dokokin da akwai hana tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe, ko kuma amfani da karfi a cikin alakar kasa da kasa, haka nan ma yin barazanar cewa za a yi amfani da karfi domin warware sabani. Domin duk wani rikice da ya hada kan iyakokin kasashe biyu ta hanyar yaki, to ya zama barazan ga zaman lafiya da sulhu na duniya.

Abinda ake so shi ne a duk lokacin da ake da sabani a tsakanin kasashe, to a yi amfani da hanyoyin ruwan sanyi wajen warware su. Idan tattaunawa ba ta iya magance sabani ba, to a je kotun duniya.

Abin  takaici  shi ne yadda bil’aadam bai fahimci hakan ba, sai da ya jefa kansa cikin bala’in yake-yake da aka zubar da jini.  Miliyoyin mutane su ka rasa rayukansu a cikin yakin duniya na 1 da na 2.Bayan hakan ne aka kirkiri MDD a 1945.

A bisa wannan dalilin, idan za a wayi gari shugaban kasar da tafi karfin soja a duniya  duniya zai aike da sojoji zuwa wata kasa, domin sace shugabanta, bisa kowane irin dalili ne, to a fili yake cewa, za a kallin hakan a matsayin rushewar dokokin kasa da kasa. Kuma mutanen za su ji cewa yanzu ana amfani da karfi a cikin alakar kasa da kasa, wato abinda Bahaushe yake kira da; ZAMANIN ANNABI SHAWO.

 Tabbas wannan ba shi ne farkon lokacin da Amurka take taka dokokin kasa da kasa ba, ta yaki kasashen masu ‘yanci da su ka hada da Panama, ta kuma kamo shugabanta kamar yadda ta yi wa Maduro na Venezuela a yanzu. Ta kuma gabatar da shi a gaban kotu,kamar yadda ta yi wa Maduro a yau.

Idan mu ka koma can baya, zuwa karni na 19, za mu ga yadda Amurkan ta mamaye kasar Canadaa fadan da take da Daular Birtaniya, mai mulkin mallaka. A 1912 Amerikan ta aike da sojojinta zuwa cikin wannan kasa mai makwabtaka da ita.A cikin watan Oktob ana 1812, sojojin Amurkan da su ka so mamaye tsaunukan Queenston, sun sha kashi a hannun mayaan kasar Canada a karkashin jagorancin Sir Isaac Brock. An ci gaba da b as u kashi har zuwa 1913.

Tarihi ya ambaci cewa har sau hudu Amurkan ta so ta mamaye kasar Cananda,amma a karshe dole ta barta a matsayin mai ‘yanci.

Wannan fandararriyar kasa wacce dokokin kasa da kasa ba su dame ta ba, ta saba kirkiro dalilai da basu su a kasa domin ta halartawa kanta tsoma a cikin kasashe mabanbabnta.  Abinda ta yi kenan Vietnam a cikin Asiya da Lao da Cambodia. A tsawon yakin da aka sani da na Vietnam, Amurka ta yi barna mai yawa ta kashe mutanen da sun  kai miliyan 3 har da doriya.

Abinda ta yi a kasar Iraki kenan, a shekarun baya, ta killace ta na tsawon shekaru masu yawa da ya haddasa mutuwar jarirari da kananan yara miliyan daya saboda cutuka da karancin abinci. Kasa mai arziki,amma aka jefa ta cikin talauci da karfi. A karshe a 2003, wannan shaidaniyar kasa ta mamaye Iraki, ta dora ikonta akan man fetur din da take da shi. Har yanzu kuwa, ita c eke cin alfanun man fetur din Iraki, domin dukkanin kudaden da aka sayar da shi a kasuwannin duniya sai sun biya ta Baitulmalin Amurka, sannan su isa ga mahukuntan Bagadaza.

Kasar da take yankin Latin wacce Amurka ta yi wa wancan irin kutse ta take dokokin kasa da kasa ita ce Panama wacce ta sato shugaban kasar Janar Manuel Noriega ta tafi da shi zuwa Amurka. Ta kirkiri hujjar cewa yana fataucin muggan kwayoyi ta shiga har cikin fadarsa ta kamo shi zuwa Amurka.

Sai dai da akwai banbanci a tsakanin abinda ya faru a Panama da na Venezuela. Shi dai shugaban kasar Panama Nowereiga ya kasance dan leken asirin Amurka da yayi aiki da CIA. Kuma a wancan lokacin an kawo karshen yakin cacar baki, sannan kuma tarayyar Soviet tana gab da rushewa. Don haka Amurka tana jin cewa ita ce za ta zama sarauniyar duniya.Kuma MDD tana taka rawa na azo a gani a wancan lokacin, da hakan ya fito fili a cikin rikicin kasar Kuwaita a 1990.

A yanzu, Amurka tana cikin yanayin koma-baya ne, tana rasa matsayin da take da shi na girman tasiri a cikin siyasar kasa da kasa. Tattalin arzikita da tasirinta  suna yin baya, haka nan kuma tana fuskantar koma baya a fagen gasa da Kasar China da take neman shige wa gabanta. Ita kuma MDD tana cikin wani yanayi dake nuni da cewa tana samun koma baya a rawar da take takawa.

 Trump ya riya cewa, ya sa an kamo Maduro ne saboda yana dillancin muggan kwayoyi da yake aikewa zuwa Amurka, suna kashe mutane. Tabbas wannan ba gasakiya ba ne, kuma idan har ace ma da gaske ne, to me ya sa yake yi wa jami’an gwamnatin kasar ta Yanzu , har da shugabar kasa barazanar cewa za su fuskanci makomar  da ta fi ta Maduro muni.!

Yana yin wannan barazanar ne saboda ya tilansta musu mika wuya ga manufofin kamfanonin Amurka da yake son su shiga cikin kasar su rika fitar da man fetur.

Wannan yana nuni da yadda karyar Trump ta fito fili akan hakikanin dalilin kamo Maduro. Amurka a karkashinsa tana son shimfida ikonta ne akan rijiyoyin man fetur da suke cikin wannan kasar.

Amurka a bisa akidar Donald Trump tana ganin cewa tara dukiya da albarkatun da suke kwance a karkashin kasa, shi ne hanyar da zai sa ta sake komawa matsayin zama mafi girman tasiri a duniya. Sai dai wannan ma ba zai zama abin dogaro ba, domin amfani da karfin da take yi zai sa kasashen da dama su bijire mata, da kuma kafa wani kawancen da a karshe zai kara mayar da ita saniyar ware.

www.hausatv.com

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted