Masu zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya, sun gudanar da ‘zaman dirshan’ a tsallaken wurin shaƙatawa na Lafayette da kuma Fadar White House a yayin ganawar Shugaba Joe Biden da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Masu zanga-zangar sun zuba jan ruwa a kan titi, suna masu cewa hakan na nuni da jinin waɗanda aka kashe a Gaza.
Kazalika sun yi ta rera taken “A kama Netanyahu” tare da nuna hoton Firaministan sanye da wata riga mai launin ruwan lemu da ke da jini, kana an yi rubutu a kai da ke cewa “A kama shi da laifin take hakkin ɗan’adam.”