Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya gana a yau alahamis da shugaban kasar Pakistan Shahbaz Sharif a gefen taron babban zauren MDD karo na 81 dake gudana a birnin NewYork na kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce shugaban ya gana da shuwagabannin kasashen duniya da dama, da kuma kafafen yada labarai.
Shugaban ya gana da babban sakataren kafafen yada labarai na kasar Amurka da tawagarsa a yau. Kuma sun tattauna kan al-amura da dama wadanda wadannan kafafen yada labarai zasu watsasu ga jama’a.
Shugaban ya amsa tambayoyi da dama kan yakin da kasar take fafatawa da Amurka da kuma HKI, da kuma dangane da halin da ake ciki a yankin yammacin Asia da kuma duniya gaba daya, musamman kan rufe mashigar ruwa ta Hurmuz.