Jakadan kasar Rasha a cibiyoyin MDD a turai ya bayyana cewa masu bincike a hukumar makamashin Nukliya ta IAEA ba zasu taba komawa JMI ba, a dia dai lokacinda Amurka tana ci gaba da barazana da kuma cewa zata sake kaiwa kasar hare hare. Ya ce a wani lokacin shugaban kasar Amurka yakin yi barazanar farwa kasar Iran da yaki sau biyu a rana guda.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mikhail Ulyanov yana fadar haka a yau alhamis a birnin Vienna, ya kuma kara da cewa, a irin wannan halin ba zai yu JMI ta amince wa wani mai bincike ya shigo kasar ba.
Banda haka jakadan ya kara da cewa, Amurka da HKI sun kai hare hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na Iran a Fordo Natanz da Esfahan a cikin watan Yunin shekara ta 2025.
A dai dai lokacinda Iran take kan teburin tattaunawa da Amurka, haka ma suka sake yi a karo na biyu a ranar 28 ga watan Fabrayru na wannan shekarar, su kuma bayyana cewa manufarsu itace kauda tsaron musuluncin da ke gudanar da kasar Iran a fili.
A wani bangare kuma hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA ta kasa yin allawadi da kai hare hare kan wadannan cibiyoyi, sannan tane neman ta sake aika ma’aikata zuwa kasar ? ta yaya Iran zata amince? Wannan dai dai ne IAEA ta sakawa Amurka da HKI kan hare haren da suka kai kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran Kenan. Ba zai yu ba in ji Ulyanov.