Kakakin kamfain jiragen sama na kasar Iran (IRANAIR) ya bayyan cewa gwamnatin kasar Turkamanistan ta hana jirgin kamfanin shiga sararin samaniyar kasar, don haka jirgin bai da zabi in banda dawowa Tehran.
Kamfanin dillancin labaran ISNA nakasar Iran ya nakalto Majid Ikhwan kakakin kamfanin jiragen sama na IranAir yana fadar haka a yau a yau Alhamis ya kuma kara da cewa, kamfanin yayi tunanin mai yuwa hakan ya faru, don haka ya fadawa dukkan fasinjoji masu zuwa Dashambe su san haka.
Banda haka kamfanin dillancin labaran Isna ya bayyana cewa ya sami labarin cewa, an dakatar da tashin jiragen Iran daga IranAir zuwa sauran kamfanonin jirage masu zaman kansu zuwa hadadden larabawa.