Ministan Harkokin Wajen kasar Masar ya bayyana cewa: Tilastawa Falasdinawa su barin muhallinsu ya zama jan layi da ba su taba amincewa da shi ba
Ministan Harkokin Wajen kasar Masar ya tabbatar da cewa: Tilasta wa Falasdinawa barin muhallinsu ta hanyar koransu daga ƙasarsu jan layi ne ga Masar, kuma Alkahira ba za ta taba bari irin wannan yanayi ya faru ba.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya bayyana a wata hira da Al Jazeera cewa: Masar ba ta ga wani matsayi mai kyau daga Isra’ila ba game da aiwatar da mataki na biyu na shirin Donald Trump kan Gaza.
Ya ƙara da cewa ɓangarorin Falasdinawa sun ɗauki matsayin da ya dace game da mika makamai, wani matsayi mai kyau.
Ministan Harkokin Wajen Masar ya kuma bayyana cewa: Alƙahira tana jiran ɗaukar mataki mai kyau daga Isra’ila game da tura rundunar sulhu ta ƙasa da ƙasa zuwa Zirin Gaza.
Abdel-Aty ya riga ya jaddada wajibcin ci gaba da matakai na gaba na yarjejeniyar Gaza da kuma share fagen tura rundunar ƙasa da ƙasa zuwa Zirin Gaza.