Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin shahadar Burgediya Janar Hussain Zarifi kwamandan dakaron da ke garin Sarayan na lardin Sitan Baluchistan a kudu maso gabacin kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto helkwatan dakarun Qud a Sarayan na bada wannan labarin a jiya Laraba. Sanarwan ta kara da cewa, Shahid Zarifi yana jagorantar wata fafatawa da yan ta’adda wadanda suke shigowa kasar daga makobtan kasashen yankin a lokacinda makaman makiya suka sameshi. Kuma bai dade ba yayi shahada.
Ta kuma kara da cewa, lardin Sistan Baluchistan a wannan karon ma ya yi asarar babban kwamanda a sarayan, kuma JMI ba zata bar bada shahidai ba, sai randa aka tabbatar da amince a yankin Sistan Baluchistan.
Kasashe makiya Amurka da HKI suna gaba gaba wajen tallafawa yan ta’adda wadanda suke son ganin bayan JMI bayan bayan samun nasara shekaru 47 da suka gabata. Lardin sitan baluchidtan ta bada dubban shahidan tun lokacin daga jami’an tsaro da kuma mutanen yankin.
Mafi yawan yan ta’addan suna shigowa kasar Iran ne daga kasashen Pakistan da kuma Afganistan wadanda suke makobtaka da Iran a wannan yankin.
Labarin ya kara da cewa a gobe Jumma’a ne ake saran za’a gudanar da Jana’izar Janar Zarifi a garin Sarayan.