Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Sabbin dabarun da sojojin Iran suka yi sun canza yanayin da ake ciki a kasa
Hukumar Leken Asiri ta Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta sanar a shafinta na sada zumunta cewa: Shirye-shiryen da dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka yi sun canza daidaiton da ke ƙasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr ya ruwaito cewa: Hukumar Leken Asiri ta IRGC ta rubuta a shafinta cewa: “Tsarin da jaruman Iraniyawa, tare da amfani da ilimin ƙasa da kyau, sun janyo dabarun yaƙi masu tsada da rashin inganci ga sojojin Amurka a halin da ake ciki. Bugu da ƙari, kashewa da kwashe sansanonin CENTCOM, da ƙauran sojojin Amurka zuwa kasar Jordan a matsayin yanki mafi aminci, sakamakon yadda ake haifar musu da hasarar rayuka, tarwatsa kayayyakin ayyukan na leken asiri da na soji sune dalilan hijiransu zuwa wurare masu nisa, da kuma ƙaura zuwa wuraren ɓuya na ƙarƙashin ƙasa, tare cusa wa al’ummar Amurka akidar cewa: Lallai manyan hasarorin da ake ci gaba da janyo wa Amurka a yankin suna kara barazana ga kasarsu.”
Saƙon ya ci gaba da cewa: “Shirye-shiryen da sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka yi sun canza yanayin fagen daga. Sun tilasta wa sansanonin soji, hanyoyin sauka, wararen ajiye makamai, jiragen sama da duk wasu kadarori komawa karkashin teku, -ciki har da jiragen Ruwan yaki na Amurka-.