Pezeshkian: Ba Zasu Mika Wuya Ga Manufofin Makiya Ba

Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika wuya ga karfi da matsin lamba ba Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya bayyana

Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika wuya ga karfi da matsin lamba ba

Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta mika wuya ga karfi ko matsin lamba ba, yayin da take ci gaba da hulda da dukkan kasashen duniya bisa girmama juna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr ya ruwaito cewa: Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya gana da Fira Ministan Bangladesh Tarique Rahman a gefen zaman Majalisar Dinkin Duniya karo na 81, inda suka tattauna muhimman batutuwa na hadin gwiwa, yanki, da na kasa da kasa.

A yayin taron, Shugaban Iran ya yi tsokaci kan dadadden dangantaka da abota tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Bangladesh, yana mai jaddada babban damar zurfafa da fadada hadin gwiwa a fannoni daban-daban.

Pezeshkian ya kuma bayyana godiyarsa ga halartar Shugaban Majalisar Dokokin Bangladesh a bikin juyayin shahadan marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, yana mai la’akari da hakan a matsayin shaida ga hadin kai da kuma kyakkyawar alakar abota tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted