Iran: Masu Yabon Amurka Zasu Farka A Makare Kan MikA Kai

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bayyana cewa kasashen da sune neman ceto daga Amurka zasu gano cewa kin karban gaskiya da

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bayyana cewa kasashen da sune neman ceto daga Amurka zasu gano cewa kin karban gaskiya da kuma saida mutunci ba zai taba karesu ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana fadar haka a shafinsa na X, kuma a maida martani ga firay ministan kasar Canada Mark Carney wanda yake goyon bayan shugaban kasar Amurka na shafe Iran daga doron kasa.

Baghaei ya bayyana cewa, wadanda suke zaton maimata maganar azzalumin shugaban zai kubutar da shi daga zalunci, wannan ba zai kubutar da su daga damkar azzalumi ba. Kuma kauda idanunsu daga ganin gaskiya, da kuma saida mutuncinsu ba zai tsiratar da su ba, amma zasu fahinci haka a makare.inji shi.

Iran wannan halin zai, maida su tsirara, babu mafaka a gaban azzalumin da ya bukace su su mika kai.

Yace Iran ta nunawa duniya yanda zasu fuskanci azzaluman kasashe, barin wannan hanyar sai duhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted