Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada A Gaza Sun Haura Zuwa 73,928

 Adadin Falasdinawa da suka yi shahada a Gaza ya kai zuwa 73,928 baya ga ragargaza duk wani abu mai amfani Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a

 Adadin Falasdinawa da suka yi shahada a Gaza ya kai zuwa 73,928 baya ga ragargaza duk wani abu mai amfani

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada a Zirin Gaza tun bayan fara yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, ya kai 73,928, tare da raunata wasu 175,030.

Kamfanin dillancin labarai na Mehr, ya ruwaito cewa: Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Zirin Gaza ta sanar a ranar Alhamis cewa: Falasdinawa biyar sun yi shahada a cikin awanni 24 da suka gabata a Zirin, daya daga cikinsu ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu.

Ma’aikatar ta kuma sanar da cewa: Falasdinawa 35 sun ji rauni sakamakon hare-haren da sojojin Yahudawan Sahayoniyya suka kai a cikin awanni 24 da suka gabata.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta kuma ruwaito cewa: Falasdinawa 1,408 sun yi shahada yayin da wasu 4,916 suka ji rauni tun lokacin da aka fara tsagaita wuta a Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted