Iran : Tawagogi 70 Daga Kasashen Waje Zasu Halarci Bikin Rantsar Da Pezeshkian

A nan Iran, tawagogin kasashen waje 70 ne ake sa ran za su halarci bikin rantsar da zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, wanda aka shirya gudanarwa da yammacin ranar Talata. Shugabannin kasashe 10 ne za su jagoranci tawagogin kasashensu zuwa Tehran domin halartar bikin, baya ga tawagogi 15 da shugabannin majalisun dokoki, da tawagogi […]

Wani Harin Isra’ila Kan Makaranta Ya Yi Ajalin Falasdinawa 30

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a zirin Gaza ta sanar a yau Asabar cewa, wani harin da Isra’ila ta kai kan wata makaranta da ke tsakiyar yankin, ya yi sanadin shahadar mutane 30 tare da jikkata wasu fiye da 100. “Makarantar Khadija, wacce ke dauke da rukunin likitocin wucin gadi a yankin Deir al-Balah, ta fuskanci […]

Kamfanin Hakar Uranium Na Faransa Ya Tafka Asara, Bayan Da Sojoji Suka Kore Shi A Nijar

Kamfanin samar da makamashin nukiliya na Faransa Orano, ya sanar da tafka asara ta Yuro miliyan 133 sakamakon matsalolin da yake fuskanta wajen gudanar da ayyukan hakar ma’adinai tun bayan zuwan sabbin mahukuntan mulkin soji a Jamhuriyar Nijar. Kamfanin ya ce ya tafka wannan asara ce a cikin watanni shida saboda matsalolin da yake fuskanta […]

Hukumar UNRWA Ta Ce: Kashi 9 Cikin 10 Na Al’ummar Gaza Sun Yi Gudun Hijira

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta “UNRWA” ta ce: Kashi 9 cikin 10 na Falasdinawa a Gaza an tilasta musu gudun hijira Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Kashi 9 daga cikin 10 na Falasdinawa an tilasta musu gudun hijira daga yankin […]

Habasha Ta Sanar Da Makoki A Kasar Sakamakon Mutuwar ‘Yan Kasar A Zaftarewar Kasa

Kasar Habasha ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa domin nuna alhini ga mutanen da zaftarewar kasa ta ritsa da su Gidan rediyon kasar Habasha “Fana” ya watsa rahoton cewa: Majalisar al’ummar kasar Habasha ta ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku domin nuna alhini da juyayi ga wadanda bala’in zaftarewar kasa ya […]

Yunkurin Hukumar Falasdinu Na Kama Kwamandan Gwagwarmaya Taimako Ne Ga ‘Yan Sahayoniyya

Yunkurin hukumar Falasdinawa na neman kama kwamandan ‘yan gwagwarmayar birnin Tul-Karam babbar hidima ce ga yahudawan sahayoniyya Mamba a ofishin siyasa na kungiyar Jihadul- Islami ta Falastinu, kuma babban jami’in kungiyar a kasar Lebanon Ali Abu Shaheen, ya jaddada cewa: Abin da hukumar cin gashin Falasdinawa ta yi na yunkurin kame kwamandan bangaren sojin Sarayal-Qudus […]

Babu Wanda Zai Iya Kafa Gwamnatin Shi Kadai Tsakanin Netanyahu Da Masu Adawa Da Shi

Masu goyon bayan fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila da ‘yan adawa ba za su iya kafa sabuwar gwamnati su kadai ba sai da kulla kawance da wani bangare Sakamakon wani kuri’ar jin ra’ayin jama’a a haramtacciyar kasar Isra’ila da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa: ‘Yan adawa da masu goyon bayan fira minista […]

Zababben Shugaban Iran Ya Bayyana Hanyar Zaben Sabbin ‘Yan Majalisar Ministocinsa

Zababben shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne mabudin warware sabanin da ke tsakaninsu Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Bin manyan manufofin siyasar kasa da shiryarwar jagoran juyin juya halin Musulunci sune mabudin warware sabanin da ke tsakaninsu. A wata hira da ya yi da […]

Iran Ta Yaba Da Cimma Daidaito Tsakanin Bangarorin Falastinawa A Zaman Beijing

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kira taron da kungiyoyin Falasdinawan suka gudanar a nan birnin Beijing a matsayin wani mataki mai kima mai kima da kuma yunkuri mai kyau. Taron da kungiyoyin Falasdinawa suka yi a baya-bayan nan a birnin Beijing ya kawo martanin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser […]

Zaman dirshan a kusa da Fadar White House don nuna goyon baya ga Falastinu

Masu zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya, sun gudanar da ‘zaman dirshan’ a tsallaken wurin shaƙatawa na Lafayette da kuma Fadar White House a yayin ganawar Shugaba Joe Biden da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu. Masu zanga-zangar sun zuba jan ruwa a kan titi, suna masu […]

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta gindaya Wa Masu Shirin Zanga-Zanga Wasu Sharudda

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta buƙaci masu shirya zanga-zangar matsin rayuwa a faɗin ƙasar da su miƙa mata bayanansu. Babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Juma’a a Abuja. Kayode Egbetokun wanda ya tabbatar da cewa ’yan kasa na da cikakken ’yancin gudanar da zanga-zanga […]

Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasdinawa a gidan kason Isra’ila

Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasdinawa shida waɗanda suka hada da mata biyu da aka sako daga gidajen yarin Isra’ila. A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu ta bayar da misali da shaidar da ta samu daga wurin fursunonin da aka sako wadda kamfanin dillancin Labarai na Anadolu ya […]

UNRWA: Fiye Da Kashi 90% Na Falastinawa A Gaza Sun Kauracewa Muhallansu

Hukumar Kula da Falasɗinawa ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) ta ce an tilasta wa Falasɗinawa tara daga cikin 10 barin gidajensu a Gaza. A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce: “An tilasta wa Falasɗinawa 9 daga cikin 10 barin gidajensu a Gaza.” Ta ƙara da cewa “iyalai suna neman mafaka […]