Hukumar lura da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen samun guguwa da ruwan sama a faɗin Nijeriya daga Yau Juma’a zuwa Lahadi. A cikin rahoton yanayi da ta fitar a jiya Alhamis a Abuja, NiMet ta yi hasashen iska mai ƙarfi da safe a yau Juma’a a wasu sassan jihohin Kano da Kaduna, tare da ƙarin wata iskar da rana a jihohin Bauchi, da Gombe, da Zamfara, da Sokoto, da Kaduna, da Adamawa, da kuma Taraba.
A yankin tsakiyar arewa kuwa, NiMet ta yi hasashen samun iska mai ƙarfi da ruwan sama da safe a wasu sassan Birnin Tarayya, da Kogi, da Benue, da Neja, da kuma Nasarawa. Da rana kuma ana sa ran guguwar a birnin Tarayya, da Filato, da Nasarawa, da Neja, da Kogi, da Kwara.
A yankin kudu, an yi hasashen ruwan sama da safe a jihohin Oyo, da Ogun, da Osun, da Edo, da Ondo, da Legas, da Akwa Ibom, da Kuros Riba, da Bayelsa, da Ribas, da kuma Delta, tare da ruwan sama daga baya da rana a dukkan yankin kudu.
A ranar Lahadi, NiMet ta yi hasashen guguwa da safe a wasu sassan jihohin Kebbi, da Kaduna, da Zamfara, tare da guguwar da yamma a jihohin Gombe, da Kaduna, da Bauchi. Bugu da kari, an yi hasashen guguwar da ruwan sama a Birnin Tarayya, da Filato, da Nasarawa, da Neja a lokacin safiya, tare da irin wannan yanayin daga baya da rana a birnin Tarayya, da Filato, da Nasarawa, da kuma Benue. An kuma yi hasashen ruwan sama da safe a wasu sassan jihohin Ondo, da Ogun, da Edo, da Legas, tare da ruwan sama daga baya a cikin rana a jihohin Osun, da Oyo, da Ogun, Ondo, da Legas, da Delta, da Edo, da Ribas, Bayelsa, da Akwa Ibom, da Kuros Riba.
NiMet ta yi kira ga jama’a da su ɗauki matakan kariya yayin da ake sa ran iska mai karfi kafin ruwan sama a yankunan da za a iya samun guguwar. Haka kuma, hukumar ta shawarci kamfanonin jiragen sama su samu sabbin rahotanni da hasashen yanayi daga NiMet domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.