Pezeshkian : Zamu Maida Hankali Kan Fadada Dangantaka Da Ketare

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa, babbar hanyar manufofin ketare na sabuwar gwamnatin kasar ita ce bude sabbin dabaru da fadada dangantakar abokantaka da sauran gwamnatoci bisa tattaunawa, hadin gwiwa, daidaito da mutunta juna. Da yake nuna godoya game da sakonni na taya shi murna da ya samu daga kasashe fiye da […]

Sudan Ta Bukaci ‘Yan Kasar Waje Su Fice Daga Birnin Khartoum Cikin Kwana Goma

Sudan ta nemi duka ‘yan kasar waje su fice daga birnin Khartoum cikin kwana 10. Kamfanin dillancin labarai na Sudan (Suna) ya ruwaito “Shugaban sashen ‘yan kasar waje da kuma shige da fice a Khartoum, Kanar Nizar Khalil, ya bai wa ‘yan kasar wajen umarnin fita daga Khartoum cikin kwana 10 domin kare tsira da […]

Iran Ta Musanta Zargin Wani Hadin Gwiwar Soja Da Yemen da Ansarallah

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta musanta zargin da Amurka ta yi ma ta na hadin guiwar soji da Yemen da kuma Ansarullah. Amir Said Iravani, jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, a wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin sulhu da babban sakataren MDD, ya yi watsi da […]

Pezeshkian: Falasdinawa za su yi nasara akan Isra’ila da izinin Allah

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar wa shugaban hukumar siyasa ta Hamas Ismail Haniyeh na nasarar da Falasdinawa suka samu a karshen yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa zirin Gaza. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya aike wa Haniyeh a ranar Laraba a matsayin hanyar […]

Putin: Hadin gwiwar Iran da Rasha zai ci gaba da kara fadada

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana aniyar kasarsa na inganta hadin gwiwa da Iran, inda ya yi kira da a kara fadada huldar dake tsakanin Moscow da Tehran a bangarori daban-daban. A yayin ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqer Qalibaf a gefen taron majalisar dokokin kasashen BRICS karo na 10 a […]

Hezbollah ta kai hari kan sansanin leken asirin Jabal al-Sheikh

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da kaddamar da hari da gungun jiragen sama marasa matuka a cibiyar binciken fasaha mai dogon zango da ke Dutsen Hermon/Jabal al-Sheikh. Harin dai ya faru ne kasa da sa’a guda bayan ministan tsaron mamaya na Isra’ila Yoav Gallant ya yi wa Labanon barazana daga Jabal al-Sheikh. Gallant […]

Za A Tafka Ruwan Sama Da Guguwa Mai Karfi A Wasu Sassan Nijeriya

Hukumar lura da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen samun guguwa da ruwan sama a faɗin Nijeriya daga Yau Juma’a zuwa Lahadi. A cikin rahoton yanayi da ta fitar a jiya Alhamis a Abuja, NiMet ta yi hasashen iska mai ƙarfi da safe a yau Juma’a a wasu sassan jihohin Kano da Kaduna, tare […]

Pezeshkian: Ba za mu sunkuyar da kawunanmu gaban wata kasa ta duniya

Zababben shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya jaddada cewa ba zai durkusa a gaban wani mai mulki a duniya ba, yana mai jaddada cewa kalaman da ya yi a baya-bayan nan ba take  ba ne, Magana ce da ya yi imani da ita. Ya ci gaba da cewa: Al’ummar Iran sun dora mini babban nauyi […]

Nasarallah: Makiya ba su cimma ko daya daga burinsu na kai hari a Gaza ba

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa: A yau Netanyahu, Ben Guerr da Smotrich, su ne ke fafutukar kare muradun kansu da tabbatar da ci gaba da kasancewa kan mulki ta hanyar ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da kashe mata da kananan yara, da rusa gidaje […]

Ministocin harkokin wajen kasashen Gabashin Afrika sun tattauna rikicin DR Congo

Tabarbarewar tsaro a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo , yanayin zaman lafiya da tsaro a halin yanzu, da kuma dangantakar da ke tsakanin kasashen, na daga cikin manyan batutuwan da ministocin harkokin wajen kasashen yankin gabashin Afirka suka tattauna a karshen taron da aka gudanar a yankin  Zanzibar na Tanzaniya. Ministocin harkokin wajen kasashen gabashin Afirka […]

Aljeriya: Ba za mu amince da duk wani katsalandan daga waje a harkokin Libya ba

Gwamnatin kasar Aljeriya ta jaddada muhimmancin cimma sulhu a kasar Libya tare da halartar dukkan bangarorin kasar Libya, a cikin tsarin cikakken aikin kasa da ya cika halastattun burinsu na kafa kasa mai bin tsarin demokradiyya. Libya dai ta fada cikin dambarwa da rarrabuwar kawuna da tashe-tashen hankula ne tun bayan harin da kungiyar tsaro […]