Babban jami’i a rundunar sojan ruwan Iran Admiral Hassan Maksud ya fadi cewa; Za a yi atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa a tsakanin Iran da Rasha ne a cikin mashigar ruwan Oman, da yankin Arewacin tekun India.
Admiral Maksud Lo ya kuma ce; Manufar yin wannan atisayen hadin gwiwar shi ne bunkasa harkokin tsaro a cikin ruwa, haka nan kuma kara karfin alaka a tsakanin sojojin ruwan kasashen biyu.
Haka nan kuma ya ce, gudanar da wannan atisayen yana da alaka da abubuwan da suke faruwa ne a cikin wannan yankin na yadda wata kasa daya tilo take son mamaye komai, haka nan kuma bayar da kariya ga jiragen ruwa na kasuwanci.
A nashi gefen Naval Captain . Alexey Sergeev na sojan ruwan Rasha ya nuna gamsuwarsa da shirye-shiryen gudanar da atisayen sojan ruwan da kuma karbar bakuncinsu da sojojojin ruwan jamhuriyar musulunci na Iran su ka yi.
Bugu da kari jami’in sojan ruwan na Rasha ya bayyana yadda alaka take a tsakanin sojojin ruwan kasashen biyu, yana mai kara da cewa; hakan yana nuni da cewa za a warware batutuwa da da dama su ka shafi kalubalen da ake fuskanta a doron ruwa.
Haka nankuma jami’in na sojan ruwan Rasha ya ce, bangarorin biyu za su gudanar da atisayen soja a doron ruwa domin kalubalantar ayyukan ta’addanci.