Yemen: Saudia Ba Zata Iya Dakatar Da Faduwar Makamata A Kanta Ba

Daya daga cikin manya manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen ya bayyana cewa gwamnatin kasar Saudia bata isa ta hana makaman yemen fadawa kan kasar ba

Daya daga cikin manya manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen ya bayyana cewa gwamnatin kasar Saudia bata isa ta hana makaman yemen fadawa kan kasar ba sai tare da biyan bukatar kasar na dauke dukkan takunkuman tattalin arzikin da kuma mutuncin kasar.

Kakakin sojojin kasar Yemen burgedia Yahyah Saree ya bayyana cewa a yau Alhamis ma, sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami samfurin bilistic da kuma jiragen kunan bakin wake a kan wasu wurare a kasar ta saudiya.

HakimAl-asad ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Laraba ya kuma kara da cewa yemen ba zata daida kaiwa Saudia hare hare ba sai tare da mayar mata da hakkinta.

Mohammad Al-Farah wani mamba a kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa gwamnatin kasar Saudia ita  ce da alhakin rikicin da ke faruwa a cikin kasar Yemen, daga arewa zuwa kudancin kasar.

 

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted