Iran Ta Bukaci Fadada Harkokin Kasuwanci Da Kasar Rasha

Ministan masana’antu, ma’adinai da kasuwanci na kasar Iran Seyyed Mohammad Atabak, ya bukaci kasar Rasha ta bada damar kara fadada harkokin kasuwanci da kasar Iran

Ministan masana’antu, ma’adinai da kasuwanci na kasar Iran Seyyed Mohammad Atabak, ya bukaci kasar Rasha ta bada damar kara fadada harkokin kasuwanci da kasar Iran ta kungiyar Iran–Eurasian Economic Union Iran-EEU.

Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da mataimakin firay ministan kasar  Rasha Alexey Overchuk.

Atabak ya kara da cewa a cikin shekaru uku da suka gabata, an sami ci gaba sosai a bunkasar harkokin kasuwanci a fannoni daban daban tsakanin kasashen biyu. Amma har yanzun akwai wasu damammaki masu yawa da fadada shi tsakanin kasashen biyu.

Ministan ya kara da cewa akwau bukatar kasashen biyu su fara ayukan gina masana’antu, zuba jari da kuma hulda tsakanin bankunan kasashen biyu.

Ya ce akwai bukatar a cire dukkan shingayen da suke hana cikken kasuwanci tsakanin kasashen biyu, wadanda suka hada da fadada hulda tsakanin bankunan kasashen biyu ta fadada aikin Shetab da Mir zuwa amfani da kudaden kasa da kasa don kasuwanci.

Sauran sun hada da hade harkokin kudaden kasashen biyu don fadada harkokin kasuwanci, aiki a kan manyamanyan injuna, da kayakin aiki, hadin guiwa wajen samar da masana’antu da sauranu.

Banda haka ministan ya bukaci a gaggauta aikin kammala layin dogo na Astara wanda yake hada kasashen biyu ta layin dogo.

A halin yanzu dai yan kasuwan kasashen biyu suna amfani da katunan banki na musamman don harkokin kasuwanci a Iran da Rasha masu suna Shatab da Mir.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted