Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare juyin musulunci na kasar iran sun sanar da cewa sun kama yan ta’adda guda 8 da ke da alaka da kungiyoyin yan ta’adda a kudu masu gabashin kasar a wani samame da dakarun kare juyin musulunci suka kai a yankin sisistan Baluchistan,
Acikin wani bayani da ta fitar a yau alhamis dakarun kare juyin sun ce cikin wadanda aka kama a kwai masu garkuwa da injiiyoyi masu kula da manyan ayyuka da ake gudanarwa a sistan baluchestan da kuma kai hari kan sojoji da yin fashi da makami da kuma tsora ta mutane a tsaikiyar lardin
Yace haka zalika yan ta’addan sun kai hari kan ofisoshin yan sanda da wasu kamfanoni da dai sauran ayyukan ta’addanci a yankin,
Jami’an tsaron kasar iran sun dauki tsauraran matakai don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin na sisisatan baluchestan, dake da iyaka da kasashen Pakistan da Afghanistan da suke da yan taadda masu yawa dake kai hari kan fararen hula da kuma jami’an tsaro a shekara bayan da suka wuce
Jama’ian tsaro sun rusa cibiyar gungun yan ta’adda a watan aprilu dake da alaka da kungiayr Jaish al-adl a yakar kasar, dake yankin sistan baluchestan kuma sun kashe yan ta’adda da dama a wajen