Kungiyar Kwallon Mata Ta Najeriya Ta Tsallake Rijiya Da Baya

sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade baa jeba yanzu dai super falconet ta daga tuta da ci 6-2

Tawagar kwallon ƙafar mata ta Najeriya Super Falcons, ta samu tikitin zuwa zagayen kusa da na kusa da karshe na gasar, bayan da ta doke Masar da ci 6-2 a wasansu na karshe a rukunin C.

 Ko da yake Najeriya bata faro gasar da kafar dama ba sakamakon shan kaye a hannun Malawi da  ci 3-2, sannan ta samu nasara da kyar a kan Zambia da ci 1-0, lamarin da ya janyo mata matsin lamba daga ƴan kallo, kasancewarta mai kare kambu.

Ya zamewa Najeriya dole ta doke Masar domin tabbatar da ci gaba da kasancewa a gasar.

Ƴar wasan gaba Asisat Oshoala ce ta fara zura wa Najeriya ƙwallo daga bugun fenariti a minti na 21, inda ta bai wa Super Falcons damar jagorantar was an, ƙwallon ta ƙara wa tawagar ƙarfin gwiwa wajen ci gaba da kai hare-hare.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Super Falcons ta mamaye wasan gaba ɗaya, inda Uchenna Kanu, Christy Ucheibe, Rasheedat Ajibade da Joy Omewa duk suka zura ƙwallaye, inda Najeriya ta ƙara yawan ƙwallayenta zuwa shida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted