Sojojin Isra’ila 2 Sun Halaka A Kudancin Kasar Labanon

Sojojin isra'ila guda biyu sun hallaka wasu guda 7 kuma sun mummunan launi

Rahotanni sun nuna cewa an sojojin Isra’ila sun sheka lahira sakamakon fashewar wani bomb da aka dana a wani gida a kudancin labanon a jiya laraba da yamma wannan itace asara mafi muni da isra’ila ta fuskata tun daga ranar 28 ga watan yuni kamar yadda hedkwatar sojin ta tabbatar.

Akwai da dama daga cikin sojojin da suka jikkata halin 4 daga cikinsu rai kwakwai mutu kwakwai, a jiya ma kafafen yada labarai na gwamnatin sahyuniya sun sanar cewa lallai wani bomb ya fashe da aka dana a wani gida a garin majdalzun dake kudancin labanon kuma yayi sanadiyar kashe sojoji 2 da kuma jikkata wasu guda 7,

Wannan yana zuwa ne bayan hare-haren da isra’ila ta kai a kudancin labanon a bangarori daban daban da tada bama bamai da rusa gidaje da rusa kabarurruka da kuma kai hare hare da jiragen sama marasa matuki,duk da yarjejeniyar da aka cimma da kuma tattaunawa da kasar labanon

Kungiyar hizbullah ta dora alhakin dukkan laifukan da isra’ila ke tafkawa a yankuna daban-daba kan gwamnatin labanon, saboda gum da baki da tayi da hakan yake bata damar ci gaba da cin karanta ba babbaka a kudancin labanon

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted