Ministan riko na tsaron kasar Iran ya ce makaman da kamfanonin kera makamai na cikin gida suke samarwa sun fi inganci a kan mafi yawan makaman kasashen yankin daga ciki har da Amurka wacce take fama da karancin makamai bayan ta share watannin tana fafatawa da JMI.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Majid Ibn Reza yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa sojojin kasar Iran a shirye suke su fuskanci duk wani sabon takala daga sojojin makiya tare da amfani da makaman da ake kerawa a cikin gida.
Ibn Reza ya kara da cewa, a duk ranar All..muna kara ganin raunin makiya, amma a dai dai lokacin sojojin kasar Iran suna kara karfi suna kuma kara shiri don fuskantar makiya tare da makaman da ake kerawa a cikin gida.
Ya ce kasashen da suke kokarin sayan makamai daga kasashen waje zasu fahinci cewa makaman JMI sun fi mafi yawan makaman da suke saya daga kasashen waje.
Wannan yana zuwa ne a dai dai lokacinda tashar talabijan ta kasar Amurka CNN ta bada labarin cewa sojojin kasar sun yi amfani da kasha 80% na garkuwan makamai masu linzami wadanda ake kira THAAD a cikin yan watannin da suka yi suna fafatawa da Iran, haka ma sun yi amfani da kimani rabin samfurin Patriot na irin wadan nan makaman.
Labarin ya kara da cewa sojojin Amurkan sun yi amfani da mafi yawan makamai masu linzami samfurin ATACMS da kuma PrSM a wannan yankin. Amurka da HKI tare sun farwa kasar Iran da yaki a ranar 28 ga watan Fabrairu na wannan shekarar da nufin kifar da gwamnatin JMI da kuma kwace iko da kasar. A yau watanni kimani 5 kenan sun kasa cimma ko guda daga manufofin soma yakin.