An Kama Ma’aikatan MOSAD 21 A Lardin Kirman Na Kasar Iran

Ministan ayyukan leken asiri na kasar iran ya bada sanarwan kama mutane 21 wadanda suke aikiwa hukumar leken asiri na HKI MOASAD a takaice da

Ministan ayyukan leken asiri na kasar iran ya bada sanarwan kama mutane 21 wadanda suke aikiwa hukumar leken asiri na HKI MOASAD a takaice da kuma wasu yan bindiga guda hudu a lardin kirman na kudu maso gabacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar leken asirin na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara da cewa, ma’aikatan Imam Zaman (a) wadanda ba’a bayyana su sun gudanar da ayyuka masu sarkakiya a lardin Kirman kafin su kai ga gano wadanda ma’aikatan MOASAD.

Labarin ya kara da cewa, hukumar MOSAD ta bukaci mutanen 21 su aiko mata wuraren tsaron sararin smaniya na JMI a cikin lardin sun aika masu dukkan hayyouin da zasu bi su gane wuraren don kai masu hare hare nan gaba.

Labarin ya kara da cewa, jami’an hukumar leken asiri na Iran sun kama wasu mutane 5 dauke da makamai irin na soje wadanda suka ma suna aikiwa wasu hukumomi daga kasashen waje don rikita kasar, tun kokarin juyin mulki na watan Jenerun wannan shekara.

Daga karshe ma’aikatar ta bukaci mutane su kira lamba 113 a duk lokacinda suka ga wadanda suke tuhuma suna aikin leken asiri a anguwanninsu a ko ina suke a kasar, don shaida masu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted