Gwamnatocin kasashen Benin da Najeriya sun kaddamar da wani shirin hadin gwiwar tsaro na musamman domin fuskantar barazanar kungiyoyin ta’addanci a iyakokinsu da ke Arewaci, matakin da ya biyo bayan yadda tsaro ya tabarbare a yan shekarun nan, inda kungiyoyin masu tayar da kayar baya suka fara bazuwa daga yankin Sahel zuwa kasashen da ke gabar tekun yammacin Afirka.
Wannan yunƙuri na hadin gwiwa na nufin toshe duk wata kofa da ƴan ta’adda ke amfani da ita wajen tserewa ko gudanar da hare-hare tsakanin iyakokin kasashen biyu.
Ƙaruwar hare-haren da aka samu tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025 ya tilastawa ƙasashen biyu fahimtar cewa babu kasa kaya da za ta iya magance wannan matsala ita kaɗai ba tare da taimakon makwabciyarta ba.
Ta hanyar wannan tsari, jami’an tsaron Benin da na Najeriya za su rika gudanar da samame tare a cikin dazuzzukan da ke tsakanin ƙasashen domin fatattakar ƴan ta’adda.
Wannan sabuwar runduna tana da alhakin kare yankunan da suka fi fuskantar barazana, musamman ma babban dajin shaƙatawa na Kainji da sauran dazukan da ƴan ta’adda ke ƙoƙarin mayar da su mafakarsu.