Newyork Times:Trump Bai yi Nasara A Yakin Da Ya Kai Wa Iran Ba

Jaridar newyorl times ta wallafa bayanai dake nuna rashin nasarar Amurka a yakin da ta kaddamar kan kasar iran

A cikin rahoton da jaridar ta buga ta bayyana cewa lalai yakin da trump ya kaddamar kan iran ya fita da ikon trump kuma duniya tana fuskantar wani babban bala’I don haka aka bukaci daukar tsauraran matakai na gaggawa don kaucema fadawa cikin bala’in

Jaridar ta ci gaba da cewa lallai trump yayi Imani cewa zai iya kifar da gwamnatin da take kai hare-hare ba kakkautawa ta sama da kuma masu zanga-zanga  sai dai abubuwan da suka faru a zahiri sun nuna akasin haka,

Ta kara da cewa lallai duniya tana fuskanta wani yaki na duniya kuma babu wanda ya sani hattama shi kanshi shugaban Amurka yiyuwar samun iko akan abubuwan da suke faruwa.

Daga karshe jarida ta yi ishara da cewa dawo da yaki da shugaban Amurka zai yi akan iran baya shuhara da samun nasara a fili, sai dai sake barkewar rikici zai kara yiyuwar tashin hankali da zai shafi wa’adin mulkinsa na biyu.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted