Iran ta bayyana cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da ta ke da kasar Oman a game da mashigarruwa ta Hormoz.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya sanar cewa akwai ci gaba a tattaunawar da nufin tsara zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci a mashigin Hormuz, yana mai bayyana yanayin tattaunawar a matsayin mai kyau.
Esmail Baghaei, ya ce tattauanwar da ake gudanarwa tsakanin kasashen biyu da ke kan iyaka da mashigin Hormuz, ta fi mayar da hankali kan ayyana hanyoyin aminci ga jiragen ruwa don shiga da fita daga mashigin.
Wadannan hanyoyin dole ne kuma a cewarsa su tabbatar da ka’idodin tsaron kasa na Iran da Oman.”
Sakamakon karshe na wadannan tattaunawar za a bayyana shi a bainar jama’a da zarar an kammala inji shi.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Masauratar Oman sun fara wani sabon zagaye na tattaunawa a farkon watan Yulin 2026 kan hanyoyin gudanarwa na mashigin Hormuz, da nufin cimma yarjejeniya da za’a aminta da ita wadda za ta ba kasashen biyu damar yin amfani da ikon mallakarsu a mashigin na Hormuz.
A lokacin taron manema labarai da ya yi a ranar Litinin, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen ya kuma jaddada, Muna neman cimma yarjejeniya kan hanyar da za ta tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa lafiya a mashigin Hormuz.
Manufarmu ita ce mu ayyana wannan hanyar da wuri-wuri, ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa da Oman.