Iraki Ta Bukaci A Zurfafa Dangantakar Binciken Ilmi Da Iran
Ammar Hakim shugaban Jam’iyyar ‘Hikma’ ta kasar Iraki ya bukaci a kara zurfafa binciken ilmi a tsakanin daliban kasarsa da JMI.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ammar Hakim yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da ministan ministan kimiya da binciken ilmi na kasar Iran Hossein Simaei-Sarraf wanda yake ziyara a kasar ta Iraki.
Bangarorin biyu sun bukaci kasashen biyu su kara fadada hulda tsakanin jami’o’iin kasashen biyu a bangren musayar fahinta da kuma ilmi.
Har’ila yau sun bukaci daliban jami’o’in kasashen biyu sun yi aiki tare don gano hanyoyin warware matsalolin siyasa tattalin arziki zamantakewa da suke addabar kasashen yankin.
Labarin ya kammala da cewa a halin yanzu, daliban kasar Iraki kimani 50,000 suke karatu a jami’o’in kasar Iran daban daban.