Yemen: Lokaci Yayi Da Mutanen Lebanon Zasu Hadakai Kan HKI

Wani babban jami’in gwamnatin kasar Yemen ya bayyana cewa lokaci yayi da mutanen kasar Lebanon zasu hada kai don fuskantar HKI. Musamman bayan kashe jami’an

Wani babban jami’in gwamnatin kasar Yemen ya bayyana cewa lokaci yayi da mutanen kasar Lebanon zasu hada kai don fuskantar HKI. Musamman bayan kashe jami’an tsaron kasar da ta yi.

Abdul Wahid Abu Ras, wanda yake rike da matsayin mataimakin ministan harkokin wajen kasar ya bayyana cewa lokaci yayi da mutanen kasar Lebanon zasu hada kai don fuskantar HKI, bayan hyare haren da sojojin yahudawan suka kai kan wata mota dauke da wasu manya manyan jami’an sojojin kasar a kudancin kasar. Yace kissan wadannan sojoji a jiya Asabar ya tabbatar da cewa gwamnatin HKI makiyar dukkan mutanen kasar Lebanon ne.

Abu ras ya bayyana haka ne jim kadan bayan da firay ministan kasar Lebanon Nawaf Salam ya zargi kungiyar Hizbullah da ci gaba da yakar HKI a yayinda gwamnatinsa take kokarin dai daita al-amura da gwamnatin yahudawan.

Y ace hare haren da HKI ta kai kan sojojin Lebanon ya nuna cewa gwamnatin kasar ta tapka kuskure babba dangane da fahintar mummunan manufofin HKI a kasar Lebanon.

Y ace lokaci bai yiba wanda fadar Baabda zata goyi bayan masu gwagwarmaya da kuma sojojin kasar don fuskantar sojojin HKI ba. ?.

Gwamnatin Lebanon mai goyon bayan kasashen yamma da HKI tana zargin kungiyar Hizbullah da laifin kissan mutane fiye da dubu 3 wanda HKI ta yi a cikin watanni 3 da suka gabata, da kuma korar wasu kimani miliyon biyu don ta ci gaba da yakar yan mamayar kasar Lebanon.

Kungiyar Hizbullah ta yi watsi da kokarin gwamnatin salami na tattaunawa da HKI a dai dai lokacin da take mamaye da kasar kuma take kissa da kuma korar mutanen kasar daga yankunansu a kudancin kasar da kuma kudancin Beirut.

Ras yace duk wani kokarin sasantawa da HKI zai sata ta ayyukan ta’addanci a kasar ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted