Yemen: Isra’ila Ta Bude Wa Kanta Dukkanin Kofofin Jahannama

Ministan watsa labaru na kasar Yemen, Dhaifullahi al-Shami ya bayyana cewa; A cikin watanni 11 na yaki a Gaza, HKI ta ka sa cimma dukkanin

Ministan watsa labaru na kasar Yemen, Dhaifullahi al-Shami ya bayyana cewa; A cikin watanni 11 na yaki a Gaza, HKI ta ka sa cimma dukkanin manufofin da ta sanar, sai dai yanzu da wannan cin kasar ya fara fitowa fili, Netenyahu da gwamnatinsa sun dauki wata siyasa ta bude yaki da dukkanin kawancen gwgawarmaya.

Dhif ya yi ishara da hare-haren da HKI take kai wa kasashen Yemen, Lebanon, Tehran, Syria da kuma Iraki, yana mai kara da cewa; Abinda HKi take son yi shi ne nuna wa duniya cewa  har yanzu tana da karfi.

Dhaif wanda tashar talbijin din al’alam’ ta yi hira da shi, ta kuma ce; Farmakin guguwar Asqa da abinda ya biyo ya tabbatarwa da duniya cewa, HKI ta ci kasa, saboda haka a zaton ‘yan sahayoniya harin da su ka kai a Tehran da kashe Isma’ila Haniyyah zai sake da wo da karfinsu.

Sai dai ministan na watsa labaru na Yemen ya ce; Shahadar da jagororin gwgawarmaya suke yi, ba abinda yake karawa gwgwarmaya sai azama da karfi,kuma ta wannan hanyar ce ake samun kai wa ga nasara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments