Mahukunta a tarayyar Nigeria sun sanar da cewa a tsakanin kananan yara 303 na makarantar Majami’ar Roman Katolika da aka sace a jihar Niger, 50 daga cikinsu sun gudu, sun kuma isa wurin iyalansu.
Masu tafiyar da makarantar ne su ka sanar da hakan a jiya Lahadi tare da kara cewa shekarun yaran da su ka gudu shekarunsu suna a tsakanin 10 ne zuwa 18.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a jihar Niger, Rev. Busul Dauwa Yohanna ne ya sanar da haka, sannan ya kara da cewa:
“A halin yanzu da akwai sauran yara 253 da malamai 12 da masu satar mutanen suke rike da su.”
A gefe daya shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinibu ya sanar da tseratar da kiristoci 38 da aka sace a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Shugaba Tinibu ya ce; Saboda kokari da kwazon rundunarmu ta tsaro a cikin kwanaki kadan da su ka gabata, an tseratar da masu ibada 38 da aka sace Eroko a Jahar Kwara.”
Sai dai babu cikakken bayani akan yadda aka ‘yanto da mutanen.
A cikin kasa da mako daya an sace dalibai a makarantun kwana na jahohi mabanbanta dake Arewa maso yammacin Nigeria da kuma tsakiyar Arewa. Bugu da kari an rufe makarantun kwana masu yawa saboda tsoron kai wa daliban hari da sace su.