Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon  na juyayin shahadar kwamanda haitham Ali Al-tabataba’i  da aka fi sani da Abu Ali wanda yayi shahada tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari  da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin berut na kasar labanon. Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar […]

Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen

Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen yayi kira ga kasar iran ta ci gaba da nuna goyon bayan kokarin da duniya ke yi wajen ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar Yamen Han Grungdbag wakilin majalisar dinkin duniya  yayi wannan kira ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen […]

Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji

Mahukunta a tarayyar Nigeria sun sanar da cewa a tsakanin kananan yara 303 na makarantar Majami’ar Roman Katolika da aka sace a jihar Niger, 50 daga cikinsu sun gudu, sun kuma isa wurin iyalansu. Masu tafiyar da makarantar ne su ka sanar da hakan a jiya Lahadi tare da kara cewa shekarun yaran da su […]

Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta

Rahotanni daga kasar Habasha sun ce dutsen na Hayli Gubbi ya fitar da kura da toka mai yawa da ta shiga kasashen Oman da Yemen. Masana ilimin kasa sun ce lokaci na karshe da dutsen ya yi aman wuta shi ne shekaru 10,000 da su ka gabata. Bugu da kari, masana ilimin kimiyya sun ce […]

Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Kwamandan Mayakan Hizbullah

Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar babban kwamandanmayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah az-Zahrah ( […]

 Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Kwamandan Jihadi Haisam al-Tabtabai

A sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Lahadi ta ce; “A cikin dukkanin alfahari Hizbullah tana sanarwa da ‘yan gwgawarmaya da al’ummar Lebanon, shahadar babban kwamanda na jihadi Shahid Haisam Ali Tabtaba’i ( Sayyid Abu Ali) wanda ya yi shahada sanadiyyar harin wuce gona da iri na yaudara na Isra’ila a  yankin […]

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 162

162-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. […]

Shugaban Kasa Ya Sami Halattar Makokin Shahadar Zahra (a) A Husainiyar Imam Khomani(q)

A dare na uku na makokin shahadar Fatiman Azzahra (s) diyar manzon All.. (s) shuwagabannin bangarorin gwamnati 3 a nan Iran sun sami halattan makakinta (s) a Husainiyyar Imam Khomanin(q) dake nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasa Dr Masoud Pazeshkiya, Alkalin alkalai Hujjatul Islam Sheikh Ibrahim Ijeyi […]

Iran Da Omman Sun Tattauna Kan Al-Amuran Yankin Da Kuma Dangantaka Tsakaninsu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Omman Badr Al-Busaidi sun tattauna a birnin Muscat babban birnin kasar Omman a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tabo al-amura da suka shafi halin da ake ciki a yankin musamman HKI da kasashen yankin, da kuma dangane da kara dankon zumunci tsakanin kasashen […]

Iran Ta Bukaci Daukar Matakan Da Suka Dace Kan Ta’asan Da HKI Ta Aikata A Beirut

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bukaci a dauki matakan da suka dace kan HKI saboda yadda take keta hurumin kasashen yankin take kuma kara zubar da jinin mutanen yankin musamman kudancin kasar Lebanon da kuma hurumin gwamnatin kasar. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nnakalto Aragchi yana fadar haka a […]

Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya Sun Yi Tir Da HKI Saboda Hare-haren Beirut

Kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a yammacin Asiya sun yi allawadai da hare-haren da HKI ta kai unguwar Dhahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiya Lahadi da yamma wanda ya kai ga shahadar mutane 5 da kuma raunata wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da babban kwamandan kungiyar […]

Najeriya: Kungiyar Yan Ta’adda Ta ISWAP Ta Sace Yan Mata 13 A Jihar Borno

Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi. Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara […]