Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Ta Mayar Wa Da Saudiyya Martani

A Saudiyya ne kungiyoyin Agaji sun sanar da gargadin gaggawa a cikin gundumar Yanbaa domin fadakar da mazauna akan hatsari da ba a bayyana hakikaninsa
Ansarullah sun kai hari akan Saudiyya

Da safiyar yau Asabar ne kungiyar “Ansarullah” ta kasar Yemen ta mayar da martani akan Saudiyya saboda harin da ta kai a wasu yankuna mabanbanta na Yemen.

Harin mayar da martanin na Yemen ya haddasa tashin gobara a wurare masu yawa,musamman a gundumar Jazan.

Bugu da kari an sami tsayuwar zirga-zirgar jiragen sama a  yankuna da dama na kasar ta Saudiyya sanadiyyar mayar da martanin da Yemen ta yi.

A jiya da dare ne dai jiragen Saudiyya su ka kai hari a tashar jiragen ruwa ta Hudaidah da kuma a garin Sa’adah dake kan iyaka.

A Saudiyya ne kungiyoyin Agaji sun sanar da gargadin gaggawa a cikin gundumar Yanbaa domin fadakar da mazauna akan hatsari da ba a bayyana hakikaninsa ba.

Hukumar da take kula da sufuri na sama ta nuna taswirar yadda ake samun sauyi a cikin kai da komowar jiragen sama da suke sauya hanyoyin da suke bi, yayin da wasu jiragen saman su ka koma inda su ka fito.

Hotunan da suke fitowa daga Saudiyyar sun nuna a kalla gobara ta tashi a cikin wurare 6,wasu daga cikinsu cibiyoyi ne masu muhimmanci. Sabon rikici ya barke ne a tsakanin Saudiyya da Yemen saboda yadda kasar Yemen din take kokarin ganin an kawo  karshen killace ta da Saudiyyar ta yi fiye da shekaru 11.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted