Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya ce Amurka ce silan duk wani rashin tsaro da ake fama da shi a mashigin ruwan Hormuz, yana mai cewa karya alkawurra da hare-haren da Washington ta kai wa Iran sun wargaza zaman lafiyar yankin.
Araqchi ya bayyana hakan ne a gefen taron Majalisar Ministocin Harkokin Waje na Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai (SCO) a Cholpon-Ata na Kyrgyzstan.
A wata tattaunawa da takwaransa na China Wang Yi sun tabo halin da ake ciki a yankin da kuma dangantakar kasashen biyu, da kuma batutuwan da suka shafi ajandar kungiyar.
Ministocin sun sake jaddada kudurinsu na kara karfafa hadin gwiwa a dukkan fannoni na muradun juna.
Sun kuma jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyoyin kasashen biyu gaba daya da kuma amfani da karfin SCO da BRICS don fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da kasashe da dama.
Araqchi ya kalubalanci karya yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka ta yi a fili, inda ya yi Allah wadai da hare-haren da Washington ta kai wa muhimman kayayyakin more rayuwa na Iran da laifukan yaki da aka aikata wa kasar.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce rashin tsaron da ake fama da shi a mashigin teku na Hormuz da kuma yankin baki daya ya faru ne kawai sakamakon karya alkawarin da Amurka ta yi kan wajibcin Iran a karkashin Sashe na 5 na yarjejeniyar fahimtar juna da aka Amince da ita a shiga tsakanin Islamabad.
A nasa bangaren, Ministan harkokin wajen Sin, Wang Yi ya ce dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Asiya yana bukatar karin hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin, yana mai sake jaddada shirin China na bayar da duk wani taimako don tallafawa wannan manufa.