Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, ya yi Allaha wadai da mamayen Isra’ila a Tuddan Golan na Siriya.
Mista Guteress ya jaddada cewa Tuddan Golan, wanda Isra’ila ta mamaye, yankin Syria ne, ya kara da cewa keta haddin da Tel Aviv ta aikata ba za a yarda da shi ba.
Ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai a kasar ta Siriya, wacce ita ce irinta ta farko da wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya kai Syria cikin shekaru 17.
Guterres ya yi kira da a “fitar da Isra’ila nan take ba tare da wani sharadi ba” daga yankin.
Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad Hassan al-Shaibani ya bayyana cewa tattaunawa da Guterres ta mayar da hankali kan sake gina Siriya, da kuma wani sabon mataki a cikin kawancen da ke tsakanin Syria da Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kuma ce ziyarar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres zuwa Damascus ta nuna sauyin da Syria ta yi zuwa matsayin “kawa” ga Majalisar Dinkin Duniya.”
Ya jaddada cewa babu wata kasa da za ta iya sake gina kanta ita kadai bayan ta fita daga mummunan rikici, ya bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya tana fatan yin aiki tare da Siriya da kasashen duniya don tallafawa makomar Damascus.
Al-Chaibani ya jaddada a lokacin taron cewa ba za a iya cimma zaman lafiya mai dorewa ba yayin da Ayyukan sojojin Isra’ila da mamaye yankinmu ba ke zama barazana kai tsaye ga tsaron yankin.