Rundinar kare juyin juya halin Musulinci ta Iran, ta ce dakarunta sun lalata jiragan yakin Amurka iri daban daban a kasa da mako biyu.
Kakakin rundunar ta (IRGC), ya ce an lalata jiragen yakin Amurka 11 da jiragai masu saukar ungulu a kasa da makonni biyu.
Janar Hossein Mohebbi ya shaida wa kamfanin dilancin labaren Tasnim a wata hira ta musamman cewa a cikin kwanaki 15, daga 6 ga Yuli zuwa 22 ga Yuli, sojojin Iran sun lalata jiragen yakin Amurka 11 da jiragen helikwafta masu saukar ungulu a sansanonin Amurka a yankin.
A hare-haren da Iran ta kai, an lalata jiragen leken asiri 17 da jiragen sama marasa matuki (wadanda 8 sabbin jiragen sama ne), da wani jirgin yaki samfarin F-15 da wani jirgin sama na P8, wani jirgin jigilar kaya na C17, da kuma jiragen sama na zuna mai 8, in ji shi.