Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar dinkin duniya ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa cikin gaggawa kan kisan gilla da azabtarwa da aka yi wa sojojin Mali da dama a yankin Gao, kuma wannan bukatar ta biyo bayan damuwar da aka nuna kan yadda ake tafiyar da rikicin yankin da kuma kare hakkin bil’adama.
Lamarin ya auku ne bayan wani mummunan harin kwantan bauna da ƙungiyoyin dakarun FLA da JNIM suka kai wa ayarin sojojin kasar a ranar 18 ga watan Yuli.
Harin ya faru ne a lokacin da sojojin ke gudanar da sintiri a yankunan da ke cikin barazanar tsaro.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe sojoji da dama yayin fadan, yayin da aka kwashe wasu da dama da rai a matsayin fursunoni.
Ƙungiyoyin ‘yan tawayen sun wallafa hotuna da bidiyoyi daban-daban a shafukan sada zumunta don nuna nasarar da suka samu a kan sojojin gwamnati.
Binciken da ake yi yana nufin tantance hakikanin gaskiyar abin da ya faru da kuma gano mutanen da ke da hannu a wannan danyen aiki. Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada mahimmancin mutunta dokokin yaki na kasa da kasa a koda yaushe.