Isra’ila na tsare da Falasdinawa 40 kusa da Nablus

Rundunar sojin Isra’ila ta ci gaba da killace garin Tell, dake kusa da Nablus, inda ta tsare sama da samarin Falasdinawa 40 a lokacin wani

clash in nablus

Rundunar sojin Isra’ila ta ci gaba da killace garin Tell, dake kusa da Nablus, inda ta tsare sama da samarin Falasdinawa 40 a lokacin wani samame da ta kai a garin dake a yankin Yammacin Kogin Jordan da ta Mamaye.

Gidan rediyon Falasdinawa ya ruwaito cewa sojojin Isra’ila suna gudanar da bincike a duk fadin garin, yayin da suke kewaye da shi a kowane bangare.

Tumda farko a ranar Juma’a, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaron kasae Israel Katz sun ba da umarnin dokar matakin soja” a kauyukan Falasdinawa a yankin Yammacin Kogin Jordan da ta Mamaye, bayan wani hari kusa da matsugunin Havat Gilad da ya kashe sojojin Isra’ila biyu tare da raunata wasu uku.

A cewar majiyoyi da shaidu, yahudawa ‘yan kama wuri zauna sun kai hari kan al’ummomin Falasdinawa da dama a Gundumar Nablus, inda suka kona gidaje da sauran kadarorin Falasdinawa.

An kashe Falasdinawa hudu a ranar Juma’a a wani hari da ‘yan kama wuri zamna da sojojin Isra’ila suka kai a garin Tell, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa.

A cewar alkaluman hukuma na Falasdinawa, an kashe Falasdinawa 87 a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye tun farkon 2026, ciki har da 21 yahudawa ‘yan kama wuri zaman na Isra’ila.

A watan Yulin 2024, Kotun Duniya ta ayyana ci gaba da kasancewar Isra’ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye da cewa haramtacce ne kuma ta umarce ta da ta dakatar da duk wani sabon aikin gina matsugunni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted