Venezuela ta fara shirinta na ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).
“Bisa ga umarnin shugabar rikon kwarya, Delcy Rodríguez, Venezuela ta sanar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, fara janyewarta daga ICC,” in ji Ministan Harkokin Wajen Venezuela Félix Plasencia a shafinsa na sada zumunta na X.
Matakin na Venezuela bai zo da mamaki ba, domin tuni Gwamnatin Caracas ta riga ta bayyana niyyarta ta ficewa daga kotun, bayan yanke shawarar daukar mataki na gaba.
Caracas ta yi Allah wadai da kotun tana mai cewa ta fi karkata ko mayar da ayyukanta kan kasashen Afirka da Latin Amurka, wanda hakan ke cutar da yankunan.
” A cewar Ministan na Venezuela, ba adalci a tsarin shari’a na duniya wanda maimakon a yi amfani da shi daidai, ana nuna rashin daidaito tsakanin mutane da kuma hana su ‘yancinsu na cin gashin kansu da ikon mallakar kansu.”
An bayyana cewa matakin Kotun na fara bincike a shekarar 2018 kan yiwuwar aikata laifukan cin zarafin bil’adama a karkashin shugabancin Nicolás Maduro ne fusata gwamnatin Caracas.
A shekarar 2025, mai gabatar da kara na ICC ya rufe ofishinsa na hulda da jama’a a Caracas, yana mai cewa Venezuela ba ta ba da hadin kai sosai ga Kotun.
Ta hanyar ficewa daga ICC, Venezuela tana bin sahun sabuwar kawarta, Amurka, wacce ke ci gaba da sukan sahihancin Kotun.
Kwanaki kadan da suka gabata, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana a jaridar WSJ cewa Amurka na da niyyar wargaza Kotun ta ICC.