Wata kotu a kasar Mali ta yanke hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru 15 bayan da aka same shi da hannu a kitsa makirci na kifar da gwamnati.
Tsohon jami’in leken asirin na kasar Mali Kanar Kassoum Goita ya fito fili ya zargi gwamnatin soja da cin hanci da rashawa. A yayin da ake yi masa shariar, ya karyata duk zargin da aka yi masa, sannan ya kara zargin gwamnatin sojan da cewa tana almubazzaranci da dukiyar kasa, kuma an azabtar da shi.
Shi dai kanar Goita yana cikin wadanda su ka taka rawa wajen kifar da gwamnatin farar hula ta shugaba Ibrahim Boubakar Keita a watan Ogusta na 2020 a karkashin jagorancin kanar Assimi Goita.
Babu alaka ta jini da ta hada shi da shugaban kasar na soja duk da kamannin sunayen iyalansu.
Kassoumu ya zama shugaban hukumar leken asiri ta cikin gida bayan kifar da gwamnatin farar hula.
A shekarar farko ta juyin mulkin, Mali ta fuskanci matsin lamba daga yankin Afirka da kuma duniya, lamarin da ya sa aka kafa gwamnatin rikon kwarya a karkashin farar hula.
Sai dai kuma 2021 Assimi Goita ya sake kifar da gwamnatin fararhular ya sake tabbatar da kansa a matsayin shugaban kasa na soja mai cikakken iko.
Mai gabatar da kara ya bukaci a daure Goita shekaru 20 da kuma wasu Karin mutane 5,sai alkalin ya yanke musu shekaru 20 na zaman gidan kurkuku.