Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas araqchi ya bayyana cewa dukkan mambobin kungiyar kasashen shanghai sun yi tir da hare-haren da kasar Amurka take kai wa kan kasar iran, wanda ya sabama dokokin kasa da kasa .
Da yake bayani a gefen taron kungiyar kasahen shanghai da aka gudanar a kasar keregystan a birnin cholpon ata a jiya juma’a ministan yace a ganawar da yayi da takwarorinsa na kasashen kungiyar dukkansu sun tir da harin da Amurka ta kaddamar akan kasar iran , yace dukkan kasashen bakin su yazo daya kan abubuwan da suka shafi kasa da kasa
Haka zalika ya ce mambobin suna neman hayoyin da zaa bi wajen tunkarar matakin da Amurka take dauka da kuma hana shi ya zamo karbabben abin da za’a amince da shi a dokokin kasa da kasa. kuma yayi gargadin cewa idan majalisar dinkin duniya ta kasa yin tir ko kuma daukar mataki, to ko ba dade ko ba jima dukkan kasashen za su iya fuskantar irin wannan barazana
Daga karshe ministan yace ganawarsa da sauran takwarorinsa na kasashen dake mambobi a kungiyar sun tattaunawa kan dangantakar dake tsakaninsu da kuma ci gaba da aka samu a yankin , sai dai batun harin da aka kai ma kasar iran shi ne ya mamaye tattaunawar ta su.